Labarai

Zuwa ga Ma’aikatan Gwamnati Musamman ma na Jihohi

Kuyi tsimi da tanaji tareda tsuke bakin Aljihun ku, an gudanar da Meeting na Rabon Arzikin ƙasa NNPC bata iya kawo ko ranyo ba, dama dai a baya Kampanin NNPC ya bayyana ma Babban Akawun ƙasar nan cewa bazai iya kawo ko sisi ba na watan Mayu da Yuni na wannan Shekarar ta Dubu Biyu da Ashirin da Ɗaya.

Bayan zaman Majalisar rarraba Arzikin ƙasa tayi zaman ta a Jiya Kamfanin Mai na NNPC bai bada ko taro ba na ɗauni ko harajin da yake kawo wa domin a had’a a raba tsakanin Gwamnatocin Jihohi da ƙananan Hukumomi dama na Tarayya.

Kazalika Kampanin na NNPC yace ba lallai bane ya Iya kawo ɗaunin watan Yuni mai zuwa, haka na nufin cewa Gwamnatocin Jihohi Talatin da Shidda da Abuja zasu raba kuɗin harajin da ƙasar ta Iya tarawa ne daga Kampanoni da sauran wasu hanyoyin samun kuɗin shiga ba na Man Fetur ba.

Da wannan zamu iya tsammatar rikicin Ƴan ƙungiyar ƙwadago a Faɗin ƙasar nan domin dai da dama daga cikin Gwamnonin ƙasar nan bazasu iya biyan Albashin Jihohin su ba, dama dai ana ta kukan cewa kudaden da ake samu daga Abuja sunyi kaɗan ga kuma kudaden shiga da Gwamnatocin Jihohi suke samu bai taka kara ya karya ba.

dama dai Najeriya tana dogara ne da Harajin da aka samu wajen saida Man Fetur da kuma Harajin Kampanoni da Ƴan kasuwa kafin a Iya rarraba Arzikin ƙasa zuwa ga Gwamnatocin ƙasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: