Kannywood

Zuwa Ga Jaruman Fina Finan Hausa

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Masu shirya fina finai, da ‘yan wasa, da masna’antun fina finan hausa sun kwashe dogon lokaci suna ikirarin fadakarwa dakuma ilimantarda jama’a suke a wannan sha’ani nasu

 

Sai dai mun kasa gane ta ina wannan fadakarwa taku take fitowa a cikin fina funanku ?

Babban abunda yake dauremin kai da wadannan mutane zasu dauko labari mai rikita kwa kwalwa, labarinda kowa yasan bazai yuyuwa Ba, amma sai suyi amfani da tasu fahimta domin ganin abun ya yuyu.

A nan zamu dauki misali da film din Gwaska, wannan film da aka shirya Wanda nake hangarsa a matsayin film dazai iya lalata tarbiyar masu kallo.

Na farko labarinda akayi amfani dashi wurin shirya wannan film labari ne da hankali ma bazai dauka Ba.

Shidai wannan film a cikinsa, an nuna hanyoyi, matakai dakuma tsarinda za’a dauka wurin yin sata ko fashi a Gidan masu hannu da shuni.

Wannan yana daya daga cikin dalilanda sukasa kasuwar wannnan masana’anta ta fara jaa da baya, ya kamata wadannan ‘yan wasa su gyara domin kawo sauyi a cikin lamuransu zai taimaka wurin kara habaka wannan masana’anta!!

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama, Jahar Kebbi Najeriya.
08146697276