Nasiha

ZUNUBI SHU, UMIN ABUNE

ZUNUBI, ZUNUBI, SHU’UMIN ABU NE!!!

Malamai masanan Allah sunce zunubi shu’uminshu’umin Ga misali zan baku:

* Idan kaga mutum yana tsakiyar aikata zunubi, sai kayi masa kwarmato, (WAI KAI GA TSARKAKAKKE) to kaci mutuncinsa kenan.. KuGA laifin cin mutuncin musulmi, yana da girma sosai awajen Allah.

* Idan kuma mutum ya aikata zunubi, sai kazo kana yi masa nasiha abainar jama’a, to Ka keta
alfarmarsa kenan. Kaima sai Allah ya keta taka alfarmar sau 70.

Kuma KAIMA sai Allah ya jarrabeka da aikata irin wannan laifin mutukar kana raye.

* Idan kuma ka Qirkiri laifi ka jinginawa wani, alhali kuwa shi bai aikata ba, to kayi masa QAZAFI..

Allah kuwa ya riga ya tsine ma masu yiwa muminai Qazafi (tsinuwar dunia da lahira) kuma alahirarma za’a tashesu ne abisa SIFFAR
KARNUKA. (Ya Allah ka tsaremu).

* Idan kuma ka ga mutum yana aikata wani zunubi, sai kaje kana gaya ma mutane, suna yin
zancensa abayan idanunsa, to hakika KACI NAMANSA, KAYI GULMARSA.

Kuma laifin masu gulma yafi na mazinata…..

* idan kuma aka baka labarin cewar ai wane barawo ne, ko mazinaci ne, ko mashayi ne, sai kai kuma ka yarda, harma kaje kana gaya ma
wasu, to Hakika kayi SHAIDAR ZUR!!

> Laifin mai shaidar Zur daidai yake da wanda yayi zina da mahaifiyarsa sau 70.

* Idan kaga mutum yana aikata laifi, sai kayi GUM da bakinka, bakayi masa nasiha ba, kuma baka Qi abin azuciyarka ba, to hakika kunyi tarayya dashi kenan acikin laifin..

To jama’a. Ina mafita? Musamman awannan zamanin da muke ciki ayanzu???

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.