Labarai

Zargin Da Ake Yi Wa Dan Sanda Abba Kyari Ko Shakka Babu Gaskiya Ne

Sharhin Alhaji Muhammad Nuhu
Don ni ma ina da korafi akan sa wanda zan gabatar a gaban Adalin Sufeto Janar na yan sanda Nijeriya. Don nayi imani zai yi mani adalci.

Dan sanda Abba Kyari ya tura yaran shi gidan mai gidana a Kaduna lokacin kotu tana yajin aiki suka kwashe kayan mai gida na har rigunar makaranta yaran sa. Wallahil Azeem ko tsinke ba su bari ba. Kuma sun karbi kudi naira miliyan 48. Sun kwashe kayan gidan sa na kimanin naira miliyan dari da sha tara, sun dauki motoci guda biyar wadanda kudin su ya kai kimanin naira miliyan 34, kuma suka tsare shi tsawon wata daya saboda suna zargin sa da ya karbi kamasho na account da hukumar EFCC ta kulle wa wani mai suna Samson, wanda ya bashi hakkin sa da ya daukar masa lauya kotu ta bude mashi account din sa.

Wanna shine laifin da mai gidana Alhaji Bashir Yahaya ya yi Abba Kyari ya kwace mashi dukiyar sa ta hanyar turo yaransa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: