Labarai

Zanga-zangar Da Aka Yi Wa Buhari A Landan Farmaki Ne Ga Arewa Baki Daya, Cewar Gwamnan Zamfara

Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kwatanta zanga-zangar da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Ingila suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin hari ne aka kaiwa Arewa.

Tun a cikin watan Maris shugaban kasa ya bar Nijeriya ya wuce Landan don a duba lafiyarsa.

Dama Buhari yana yawaita zuwa Landan tun da ya hau kujerar shugaban kasa a 2015.

Wasu ‘yan Naieriya mazauna Landan sun yi wa Buhari zanga-zanga bisa yajin aikin da likitoci suke yi a Nijeriya.

A wata takarda da ta fito ranar Alhamis wacce Matawalle ya tura ya bayyana zanga-zangar a matsayin al’amari da wasu suka dauki nauyi, kuma wadanda suka shirya basu da wayewa.

Ya kuma ja kunne akan kaiwa ‘yan Arewa hari da kuma masana’antun su a kudu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: