Labarai

Zan Yi Iya Kokarina Don Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda A Nijeriya, Cewar Janar Faruk Yahaya

Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa Shugaban Sojojin Nijeriya Janar Farouk Yahaya ya jagoranci zaman majalisar sojojin Nijeriya tare da manyan sojoji a karon farko tun bayan maye gurbin marigayi Janar Attahiru ya yi, inda suka tattaunawa matsalar rashin tsaron dake addabar kasa.

A yayin zaman majalisar, Janar Farouk Yahaya ya tabbatarwa da dakarun sojojin Nijeriya cewa zai daura daga inda marigayi Janar Ibrahim Attahiru ya tsaya wanda ya rasa rayuwar shi a daidai lokacin da yake kokarin samar da tsaro a cikin Nijeriya.

Janar Farouk Yahaya ya ci gaba da bayyana cewa tabbas burina zai cika kafin inbar kan wannan kujerar ta COAS domin ayanzu haka banda wani burin da yawuce inga bayan duk wani dan ta,addan dake rayuwa a cikin Nijeriya amma hakan bazai tabbata ba saida sadaukarwar ku.

“Kamar yadda na san kun san cewa Nijeriya na cikin wani hali ta fuskar tsaro wanda hakan ke bukatar jajircewar ku domin ganin zaman lafiya yadawo cikin Nijeriya.

A yayin jawabin Janar Farouk Yahaya ya yi kira ga manyan hafsoshin Nijiriya da su tashi tsaye don ganin an magance matsalar tsaro a yankunan Nijeriya baki daya.

Akarshe janar Farouk Yahya yace insha Allahu a karkashin shugabancin sa rundunar sojojin Nijeriya za ta yi aiki tukuru domin ganin cewa ta sauke nauyin dake wuyan ta na samar da cikakken tsaro a cikin lungu da sakon Nijeriya

Muna rokon Allah ya daura dakarun sojojin Nijeriya akan ‘yan ta’addan Nijeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: