Labarai

Zan Tsaya Takara A Shekarar 2023 – Attahiru Jega

Daga Tukur Sani Kwasara
Rahotanni daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar PRP ne domin ya bada gudummuwarsa a siyasance.

Jega ya kara da cewa zai tsaya takara a zaɓen 2023 dake tafe amma ya zuwa yanzun bai yanke shawara a kan mukamin da zai tsaya takara ba.

Farfesa Jega ya faɗi haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da sashen Hausa na BBC a karshen makon da ya gabata.

Tsohon shugaban hukumar zaben INEC yace jam’iyyar APC da ta adawa PDP ba su da kwarewar cigaba da jagorancin ƙasar nan a yanzu. “Manyan jam’iyyun kasar nan biyu APC da PDP ba su cancanci ci gaba da jagorancin kasar ba, basu da kwarewar da ake bukata.” “Ina kira ga yan Najeriya (kasar da tafi yawan jama’a a Nahiyar Afirka) da kar su sake zaɓen su a babban zaben 2023 dake tafe”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: