Zan Sayar Da NNPC Ko Za A Kashe Ni —Atiku

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasa za ya saida kamfanin man Najeriya, NNPC.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da yan kasuwa a jihar Legas a jiya Laraba.

Talla

Atiku ya ce “Zan tabbatar da sayar da NNPC ko da za su kashe ni.”

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

Talla
1 of 661

Atiku Abubakar dan kasuwan ne kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007.

Atiku Abubakar yana jawabin a lokacin da ya bayyana cewa ya fita daga jam'iyyar APCHakkin mallakar hotoTWITTER/ATIKU ABUBAKAR
Image captionAtiku Abubakar yana jawabin a lokacin da ya bayyana cewa ya fita daga jam’iyyar APC

A watan Nuwamban 2017 ne ya kaddamar da yakin neman zabensa da alkawarin cewa zai hada kan ‘yan Najeriya da samar da ayyukan yi.

Atiku Abubakar dai ya bar jam’iyar APC inda ya koma PDP a ranar 3 ga watan Disamba na 2017.

Wannan shi ne karo na biyu da zai yi takarar zaben game-gari tun bayan da ya sauka daga mataimakin shugaban kasar Najeriya a 2007.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: