Zai kasance babban kuskure gareni in cigaba da amfani da motar da aka bani don inyi kamfen, tunda dai na bayyana cewa bazanyi kamfen din ba.
Hatta yan kudaden kashewar da aka bani duk sunanan a lissafe kuma zan mikasu in sha Allah zuwa gobe.
Bazai yiyu in hana mutane hasashe akan wannan lamari ba, sai dai dole akwai cikakkiyar gaskiyar lamarin dani Biyora na sani suma wadanda suka bani daga gidan dana koma a kwanakin baya suka sani.
Na yanke shawarar dawowa tafiyata ta baya ne saboda wasu dalilan da nake ganin ta haka ne kawai zanfi samun saukin gudanar da rayuwata, koda kuwa naci gaba da yawo akan babur dina ne, tuni na saka an gyaramunshi don cigaba da zirga zirga akansa kamar yadda na saba a baya.
- Advertisement -
Kalubale dole na sake fuskantarsa a yanzu kamar yadda na fuskanta a baya may be yafi na baya yawa.
In sha Allah bayanai zasu fito ta yadda kowa zai fahimci dalilin dayasa na yanke wannan sabuwar shawarar.
A shirye nake na jingine siyasa gaba dayanta idan har mutane basu fahimta ba.