Labarai

Zan kare rayuka da dukiyoyin kabilar Igbo a Katsina – Sarkin Katsina

 

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir, ya bayyana cewa zai kare lafiya da dukiyoyin kabilar Igbo da sauran kabilu mazauna jihar Katsina. Ya ce Najeriya za ta ci gaba da kasancewa kasa daya, mai al’umma daban, amma dunkile wuri daya.

Sarkin ya yi wannan kalami ne a ranar Jama’a lokacin da ya ke wa shugabannin kabilar Igbo da na sauran kabilu, mazauna Katsina a fadar sa.

“Ina magana ne dangane da wani wa’adi da aka ce wata kungiya ta bai wa Igbo mazauna Arewa wai su fice daga yankin. Masu bayar da wannan gargadi ba su yi mana fatan zaman lafiya.

Mu a nan Katsina, a shirye na ke na kare rayuka da dukiyoyin kowane dan Najeriya, ko da kuwa zan sadaukar da raina. Inji Sarkin Katsina.

Daga nan Sarki ya roki dukkan mazauna jihar Katsina cewa kada su tada hankulan su, domin Majalisar sa da kuma gwamnatin jihar Katsina, za su yi duk abin da ya dace domin tabbatar da zaman lafiya.

” Dukkanin ku ‘yan Najeriya ne, wasun ku ma a nan Katsina aka haife su. Ba ku da wurin da ya fi Katsina.

“Don haka ku ‘ya’yan na ne, Katsina gidan ku ne, kowa ya wataya duk inda ya ke so.”