Labarai

Zan Iya Warkar Da Buhari Idan Anaso Ya Samu Lafiya

Kamar Yadda Na warkar Da IBB

Limamin addinin Satguru Maharaj yace zai iya warkar da shugaban kasa Muhammadu Buhari idan har zai yarda ya zo majalisar sa domin haka.

Satguru Maharaj Ji ya ce shine ya warkar da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida a lokacin da ya ke shugabancin Najeriya a wancan lokacin.

Limamin ya fadi haka ne da ya ke zantawa da manema labarai a Legas.

Shugabancin Kasa ba wasa bane, dole ne mu yi yadda zamuyi don ganin ya sami lafiya.

 

Idan da Buhari zai yarda idan ya dawo, ya ziyarce ni domin warkar dashi cutar da yake fama dashi kamar yadda nayi wa tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da ya ke ciwon kafa. Amma da ya musanta haka da ga baya ai gashi ciwon ta dawo.”

“Ko a wancan lokacin da Buhari zai tafi kasar Britaniya nine kadai na ce zai dawo kuma ya dawo.

Saboda haka ni zan iya warkar dashi idan da zai zo domin haka.”

Bayan haka kuma Satguru Maharaj Ji ya ce jam’iyyar APC ce za ta ci gaba da mulkin kasa Najeriya har bayan 2019 sannan ya yi kira ga malaman jami’o’in kasar nan da su mai da wukan su koma teburin tattaunawa da gwamnati.

Me Zakuce?

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.