Labarai

Zan iya Gayyato Manyan ‘Yan Ta’adda Daga Sassa Daban-daban Na Duniya Domin Su Tarwatsa Nijeriya

Inji Shugaban ‘Yan Ta’addan Daji Masu Hallaka Al’umma A Jihar Zamfara

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Shugaban ‘yan ta’addan daji masu hallaka al’umma a cikin jihar Zamfara, Turji, ya yi barazanar gayyatar mayakan `yan ta’adda daga kasashen waje don tayar da zaune tsaye a Nijeriya a gaban Sheikh Ahamad Mahmood Gumi.

Idan ba a manta ba, Sheikh Ahamad Gumi ya ziyarci ‘yan ta’addan daji masu hallaka al’umma a cikin jihar Zamfara domin tattauna yadda za a samar da zaman lafiya a cikin jihar baki Daya.

Shugaban ‘yan ta’addan wanda ya addabi al’umma a yankin Arewa maso Yamma, Kachalla Turji, ya ce kungiyarsa na iya yin kira ta samu goyon bayan kasashen waje don lalata Nijeriya.

An ji Turji a cikin wani faifan bidiyo da aka yada a kafar Facebook suna tattauna korafe-korafen da suka ci gaba da kashe-kashe, satar mutane da kungiyoyin masu satar shanu a yankin.

Turji ya ce kungiyar su ta halarci wannan tattaunawar ne saboda malaman addinin Musulunci ne suka shirya shi.

Wani daga cikin ‘yan bindigan yana rataye da RPG a yayin zaman, wanda ya gudana a yankin Shinkafi na jihar Zamfara, inda kungiyoyin ‘yan ta’adda ke ta addabar al’ummar yankin ta hanyar kashe jama’a tare da karbe dukiyoyin su.

Ziyarar ta Gumi na daga cikin kokarinsa na samar da zaman lafiya da kuma wayar da kai ga al’ummomin Fulani da kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin Arewa maso Yamma.

#Rariya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: