Kannywood

Zan Hallaka Kaina Cewar Umme Zee Jarumar Kannywood

UMMI ZEE-ZEE: Duk Wanda Bai Ji Bari Ba, To Zai Ga Hoho..

Daga Datti Assalafiy

Ummi Zee-Zee tsohuwar tauraruwar Hausa fim wacce duniya ta kare mata, ta wallafa takaitaccen jawabi a shafinta na Instagram cewa zata hallaka kanta.

Tsohuwar tauraruwar tace don Allah kada kowa ya tambayeta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki na kisan kanta, tace abinda kawai take bukata shine addu’ah, kamar yadda zaku gani ta rubuta da yaren turawan mulkin mallaka.

A gaskiya ni Datti Assalafiy banyi mamakin jin haka da wannan matar ba, domin ina da cikakken masaniya akan tsarin rayuwarta da kuma halin da take ciki, sai dai bata bayyana ba a fili, don haka nima ba zan bayyana ba.

Irin wannan rayuwar abin kyama ne, tun farko Malamai da mutanen kirki na basu shawara da yin nasiha su ji tsoron Allah, su canza tsarin rayuwarsu amma basa ji, sun zabi rayuwar son zuciya, gashinan duniya ta kaisu ta baro.

Duk takamar mace budurwa da cikar dirinta da kyawun surarta wanda yake jan hankali da tayar da sha’awar maza, a kwana a tashi idan tana raye sai ta riski shekarun tsufa, sai ta kai matakin da inda zatayi tsirara haihuwar uwarta a kan idon namiji ba zaiji sha’awarta ba saboda tsufa.

Sana’ar Hausa film ko sana’ar bin maza ga mace Musulma ba alheri bane ko kadan, kuma ba abune mai kyau ba, domin inda sana’ar Hausa film abune mai kyau da munga manyan daraktoci suna saka matansu da ‘ya’yansu da kannensu a ciki, gidan mijin nan dai shine rufin asiri, kuma duk tsananin wahalar gidan miji yafi zaman banza ba aure alheri.

Ita mace rayuwarta gaba daya abin tausayi ne, duk abinda zata samu na dukiya da duk mukamin da zata rike darajarta da mutuncinta da jin dadin rayuwarta wallahi yana gidan mijinta na aure, amma mafi yawancinsu basa ganewa, gurbatattu ‘yan Boko aqeedah sun ribaci zukatansu.

Muna tausayawa rayuwar wannan mata, hakika inda tana da tarbiyya na addini da bata fadi haka ba, domin duk matsalar da ke damunta zata samu mafita a Qur’ani da Hadisi, amma sai gashi ta zabi tayi mummunan karshe irin wanda limamanta yahudu da nasara ke yi wajen kashe kansu idan duniyar ta musu kunci.

Muna yiwa wannan matar nasiha a matsayinta na Musulma, ta sani a Musulunci duk wanda ya kashe kansa sakamakonsa wutar jahannama ne, duk matsalar dake damunki akwai mafita a addinin Musulunci.

Sannan daga karshe ina baki shawara ki tuba tsakaninki da Allah, ki rufe wannan gidan naki, kiyi gaggawan canza kawayenki da wadancan abokan huldar naki, inda hali ma ki canza gari, ki nemi miji kiyi aure, zaki samu sassauci Insha Allah.

Yaa Hayyu Yaa Qayyum Ka bawa wannan matar mafita na alheri, Yaa Allah Ka dubeta da idon rahamarKa. Amin.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement