
Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku yace zai daukaka kara akan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke wanda ya soke zaben sa a matsayin gwamnan jihar.
A ranar Asabar din nan ce kotun sauraron karrakin zabe ta jihar Taraba ta soke zaben gwamnan jihar ta Taraba tare da bada umarnin rantsar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan a matsayin gwamnar jihar.
Alkalin kotun Justice Musa Danladi jam’iyyar PDP ba ta gudanar da cikakken zaben fidda gwani ba kafin ta tsayar da dan takararta Darius Ishaku wanda hukumar zabe INEC ta baiyana a matsayin wanda ya lashe zaben.
Mai baiwa Gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai Sylanus Giwa ya bukaci jama’ar jihar su kwantar da hankalin su yana mai cewa gwamnati za ta daukaka kara akan hukuncin.
A nasa bangaren, Mahmud Abubakar Magaji lauyan da ke kare Hajiya Aisha JUmmai Alhassan ya baiyana hukuncin kotun da cewa gaskiya ce tayi halinta.
Add Comment