Kannywood

Zan Cigaba Da Yin Film Din Nollywood Duk Da Nadawo Kannywood – Rahama Sadau

Rahma Sadau ta dawo fim tun bayan da kungiyar Moppan ta kore ta daga kannywood. bisa wata waka da suka yi ita da mawaki Classiq.

Bayan Jaruma Rahma Sadau ta bayar da hakuri akan laifin da ta aikata.

Kungiyar Moppan ta sanarwa duniya cewa ta dawo da jaruma Rahma Sadau Kannywood.
Jarumar ta bayyanawa jaridar Premium Time cewa: dawowar ta kungiyar kannywood ba zai hanata yin fina finan kudanci ba (nollywood).

Domin cikar jaruma shine a santa aduniya.
Acewar Rahma Sadau: Ni dama burina in zama jaruma ta duniya gaba daya, ba kawai jaruma a hausa fim ba.

Misali, Ali Nuhu da Sani Danja matsayinsu nake so in kai a harkar fim. ba wai kudi ko wata kadara ba, a’a, kawai a san ni aduniya kamar yanda aka san su.
Kuma duk suna yin fina finan kudanci, dan haka ba gurin sunan su Ali Nuhu da sani danja basu shiga ba. Nima haka nake so in zama.

Inji Rahma Sadau.
Zata ci gaba da yin fim na kudanci inji Rahma Sadau.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.