Labarai

Zan Biya 500,000 Ga Duk Wanda Ya Tona Asirin Masu Tada Zaune Tsaye – Gwamna Yahaya Bello

Gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello ya ce gwamnatin sa zata biya lada ga duk wanda ya fallasa masu yada jita jita da zummar ta da zaune tsaye a jahar.
Gwamnan yace zai biya Naira na gugan Naira 500,000 ga duk wanda ya samarwa hukumomi bayanan da za su sa a kama masu tayar da zaune tsayen.
A wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Petra Onyegbule, ya bayyana cewa hakan ya zama dole, duba da yadda irin wannan ta’ada ta zama ruwan dare a jahar.
Gwamnan ya ce yana fatan wannan abu zai taimaka wajen rage faruwar laifuffuka da kuma ayyukan wadanda ‘yan siyasa ke biyan su domin su yada jita jitan da ke haifar da tashin hankali.
Duk da cewa wasu na ganin wannan abu ya yi, akwai da dama da ke ganin cewa hakan zai iya tauyewa mutane ‘yancin su na fadin albarkacin bakin su.
Toh sai dai mai taimakawa gwamnan akan harkokin sabbin kafafen yada labarai ya jaddada cewa babu hatsarin hakan za ta faru a karkashin wannan mataki.