Zamu kawo Shekau nan da kwani 40 kamar yadda mukayi alkawari – Rundunar soji

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

– Rundunar soji sun yi alkawarin kamo Shekau kamar yadda Buratai ya umurce su

– Ta ce bata taba sanar da cewa an kashe shi ba a baya

– An yaba ma shugaban hafsan soji kan aikinsa

Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kaddamar da umurnin da Tukur Buratai ya ba ta na kamo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, a raye ko a mace cikin kwanaki 40

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 906

A cewar Channels TV, Birgediya Janar Sani Usman wanda ya kasance kakakin rundunar sojin ne ya tabbatar da hakan a Buniyadi, jihar Yobe.

Hakan ta kasance ne a lokacin wani ganawar sirri da Buratai yayi da rundunar musamman rundunar sashi na 27.

Sojojin sun yaba ma Buratai kan aikinsa da kuma kulawarsa sannan kuma sun yi alkawarin cewa zasu kama Shekau cikin kwanaki 40.

A halin yanzu, Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yawan hare-hare da ‘yan ta’addan Boko Haram ke kaiwa a kasar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.