Siyasa

Zamfara: Matasan APC Sun Zargi Sanata Marafa Da Hargitsa Jam’iyyar

Daga Yusuf Shuaibu,
Matasan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara sun yi nuni da cewa Sanata Kabiru Garba Marafa yana kokarin lalata jam’iyyar a jihar ta hanyar gudanar da wasu ayyukan da suka saba wa jam’iyyar. Matasan jam’iyyar APC sun bayyana cewa Sanata Marafa ne ya hana jam’iyyar kafa gwamnatin a shekarar 2019 bayan ya kai karar jam’iyyar a gaban kotun kali, wanda ya yi sanadiyyar jam’iyyar PDP ta samu mulki.

Sanarwar da suka fitar mai dauke da sahannun shugaban matasan jam’iyyar APC, Alwan Hassan ya bayyana cewa kalaman Sanata Marafa zai iya hargitsa jam’iyyar tare da kawo rarrabuwar kai.

“Mutumin da kai jam’iyyar kotu a shekarar 2019, wanda hakan ya janyo jam’iyyar APC ta rasa mulki a Jihar Zamfara, haka kuma kalamun da Sanata Marafa yake furtawa za su iya hargitsa jam’iyyar, wanda ya kamata ‘yan siyasa su ja kunnansa.

“Wannan abun ban mamaki ne da fargaba a ce Sanata Marafa wanda a ko da yaushe yake watsi da dukkan dokokin jam’iyyar APC kamar na yadda tsarin dokar jam’iyyar ya bayyana cewa gwamnonin da ke kan kujerar mulki su ne shugaban jam’iyyar.

“Wannan daya daga cikin abun mamaki na dalilin da ya sa Marafa ya dauko hanyar ruguza jam’iyyar tun kafin zaben shekarar 2023.

“Ko shakka babu, Sanata Kabiru Marafa ya rasa darajar daga cikin mambobin wannan jam’iyyar tamu. Wannan yana adawa da duk wani kokari da na shugabancin jam’iyyar karkashin shugaban ruko kuma gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi wajen dawo da darajar jam’iyyar a Jihar Zamfara, amma sai da ya kalubalanci wannan lamari.

“Wannan ba abin da za a kuma lamunta ba ne, saboda ya kai jam’iyyar kotu a shekarar 2019 wanda hakan ya haddasa wa jam’iyyar asara a cikin jihar. Ya kamata a kori Sanata Marafa daga cikin wannan jam’iyyar. Mun fahimci cewa jam’iyyar tana fuskantar ayyukan cin amana daga wajen Sanata Marafa, wannan lokaci ne da ya kamata a dauki tsauraran mataki a kan kokarin ruguza jam’iyyar da Marafa ya yi.

“A matsayinmu na matasan jam’iyyar, ba za mu lamunci duk wani cin kashe na wannan jam’iyyar tamu daga wajen Sanata Marafa ko kuma duk wani mutum. Domin haka, muna kira ga Sanata Kabiru Marafa da ya daina ayyukan da za su janyo ruguza jam’iyyar APC ya kuma fahimci cewa babu wani dan siyasa da zai iya tarwaza wannan jam’iyyar komin mabiyan da yake da su.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement