Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana zakka a matsayin wani makami da za’a iya amfani da shi wajen yakar talauci a tsakanin al’umma.
Basaraken a wajen taron raba zakka wanda gidauniyar bayar da tallafi na Jaiz ta shirya aka kuma gudanar a fadarsa da ke Kano, yace idan har aka tsara rabon zakka yadda ya kamata, zai rage yawan talauci a kasar.
Akalla mata 100 ne suka amfana daga rabon kayayyaki kamar su kekunan dinki da injin nika, firinjin daskarar da kankara da kuma kudade.
Sarki Sanusi ya tuna cewa a lokacin zamanin wasu kalifofin annabi bayan mutuwar manzon tsira annabi muhammad, babu talakawa a karninsu da suka cancanci karban zakka saboda wadanda aka rarraba a shekarun baya yasa duk sun zamo masu dogaro da kai.
- Advertisement -
A cewarsa ana tura kudaden ne zuwa sauran kasashen waje. Sarkin ya jadadda cewa addinin Islama addini ne da ke gudana a aikace.
Sarkin ya yabawa bankin Ja’iz kan samar da gidauniyar tallafawa gajiyayyu da kuma kawo rabon da suka yi Kano tare kuma da zabar mata a matsayin wadanda za su amfana daga shirin.
Sarki Sanusi ya bukaci wadanda suka amfana daga shirin da su yi amfani da kayayyakin da aka rarraba masu wajen dogaro da kansu.