ZABEN 2023: Jerin Gwamnonin Arewa Biyar Da Suka Ce Lallai Mulki Sai Ya Koma Yankin Kudancin Nijeriya

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Comr Abba Sani Pantami
Duk da cewa da sauran shekaru biyu a yi zaben shekarar 2023, an fara muhawara kan yankin da mulki zai koma bayan karewar wa’adin shugaba Muhammadu Buhari.

Har yanzu, manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya All Peoples Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) basu bayyana yankin da zasu baiwa tikitinsu ba.

Amma ana hasashen cewa tun da dan Arewa ke mulki yanzu, ya kamata mulki ya koma kudu a 2023.

Jerin wasu gwamnonin Arewa Biyar sun bayyana cewa wajibi ne mulki ya koma kudancin Najeriya a shekarar 2023.

Gasu kamar haka;

1. Babagana Zulum (Borno)

A bikin murnar ranar haihuwan tsohon dan takaran gwamnan Rivers, Dakuku Peterside, Zulum yace: “Tsarin kama-kama alkawari ne mukayi, saboda hakan akwai bukatar mulki ya koma kudu.”

2. Nasir El-Rufai (Kaduna)

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce mulki ya koma kudu a 2021.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 782

Yace: “Daga Kudu ya kamata shugaban kasa ya fito a 2023; ban goyon bayan dan Arewa ya zama shugaba bayan Shugaba Muhammadu Buhari saboda yarjejeniyar siyasar Najeriya.”

3. Abdullahi Umar Ganduje (Kano)

Hakazalika, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce duk da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi tsarin kama-kama ba, akwai bukatar a yi amfani da shi don samun nasara a zabe.

4. Aminu Bello Masari (Katsina)

Gwamna Aminu Masari na Kastina ya yi kira ga kama-kama a 2023.

A cewarsa, don adalci da nuna daidaito, ya kamata a baiwa kudu damar mulkan Najeriya a 2023.

5. Abdullahi Sule (Nasarawa)

Kwanakin baya, gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna goyon bayansa ga tsarin kama-kama. Ya ce akwai bukatar shugaban kasa yazo daga kudu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: