Zaben 2019 ya bar baya da kura


0 101

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rikicin siyasa ya kara kamari a Najeriya tun bayan zaben shugaban kasa da aka bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe.

Babban jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi watsi da zaben shugaban kasa inda tuni ta kalubalanci sakamakon da ta ce an yi magudi a kotun sauraren karar zabe.

Soke zaben gwamna a wasu jihohi da aka yi na wasu mazabun kananan hukumomi ya kara haifar da rudanin siyasa a Najeriya.

Rahotanni daga masu sa ido a zaben kasar sun bayyana damuwa kan yadda rikici da tsoratarwa da sayen kuri’u suka mamaye zaben gwamnoni.

Yayin da wasu ke ganin an samu ci gaban dimokuradiyya a Najeriya, wasu kuma na ganin har yanzu babu wani abin da ya sauya daga matsalolin zabe da aka saba gani a zabuka a kasar.

Zargin Magudi

Atiku AbubakarHakkin mallakar hoto@ATIKU

Tun daga zaben shugaban kasa zuwa na gwamnoni jam’iyyun hamayya ke korafin an yi magudi.

Dan takarar babbar jam’iyyar hamayya wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya yi zargin an yi magudi inda ya ce ba zai amince da sakamakon zaben ba.

Tuni ya shigar da kara a kotun sauraren karar zabe inda yake kalubalantar hukumar zabe INEC da jam’iyyar APC da dan takararta shugaba Buhari da aka bayyana ya lashe zaben shugaban kasa.

A cikin koken da ya gabatar tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi ikirarin cewa shi ne ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu bisa wasu hujjoji da ya bayyana a cikin kokensa.

Sai dai Jam’iyyar APC ta ce a shirye ta ke ta kalubalanci PDP a Kotu.

Malaman ZabeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Jam’iyyar PDP ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta da nuna goyon baya ga jam’iyya mai mulki bayan soke zabukan wasu jihohin da ta yi ikirarin cewa ta yi nasara.

Sai dai APC ta yi watsi da zargin inda mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labaru Garba Shehu, ya ce babu ruwan shugaba Buhari da zabe.

Ya ce hukumar INEC ita ce ke da wuka da nama a kan duk wani zabe da za a gudanar.

Shugaban ya ce ‘ya’yan jam’iyyar APC din su je su nemi kuri’a a wurin jama’a shi ba zai sa hannu ba.

Ya zargi wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulkin kasar da kokarin ganin shugaban kasar ya yi amfani da karfinsa wajen murde sakamakon zaben.

Kungiyoyin fararen hula da suka sa ido a zaben na Najeriya sun yi kiran a kafa kwamiti na musamman domin binciken yadda aka gudanar da zaben gaba daya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Rikici

Zabe a NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

A tarihi, zaben gwamnoni ya fi jan hankali a Najeriya saboda tasirinsu ga siyasar kasar.

An kasa gudanar da zaben na gwamna a wasu yankunan jihohin saboda rikici.

Wasu kungiyoyin da suka sa ido a zaben nuna damuwa kan sahihancin sakamakon zaben wasu mazabu da aka samu rikici.

Cibiyar bunkasa dimokuradiyya ta CDD ta ce an yi amfani da ‘yan daba domin tsorata masu zabe da ‘yan jarida a wasu manyan mazabun da ke da tasiri a zaben Kano.

Hankali ya fi karkata a Kano da Sokoto da Bauchi da Filato da Benue, jihohin da aka sake zaben wasu mazabu na kananan hukumomi.

Siyasar Kano ta fi jan hankali, saboda girman hamayya tsakanin manyan jam’iyyun siyasa guda biyu APC da PDP.

Wasu ‘yan daba dauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya kan mazabu daban-daban da ke garin Gama na jihar Kano, inda suka hana gudanar da zabe.

Garin na Gama na da masu zabe kusan 40,000 kuma shi ne wurin da aka fi fafatawa a zaben da ake gudanarwa a karamar hukumar Nasarawa da ke jihar ta Kano.

Wakilan BBC da ke garin sun ga yadda ‘yan dabar dauke da makamai suka rika tsorata masu kada kuri’a da kuma korar su.

Sai dai hukumar INEC da kuma rundunar ‘yan sandan kasar ba su ce komai dangane da lamarin.

Sayen kuri’u

Wata babbar matsala ita ce yadda aka ci kasuwar saye da sayar da kuri’u ba tare da kakkautawa ba a zaben Najeriya.

Hukumar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wasu da take zargi da laifin sayar da kuri’un, kuma ta ce tana iyakar bakin kokarin ta wajen hana irin wannan dabi’a.

Tawagar BBC da ke aikin dauko shirye-shiryen zabe a Kano, ta ga yadda ta karkashin kasa ake sana’ar saye da sayar da katunan zabe.

A lokacin zaben gwamnoni da ya gabata, wasu hotuna da bidiyo da ke nuna yadda ake amfani da kudi wajen sayen kuri’a sun rinka yawo a shafukan sada zumunta.

Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati na EFCC da ta yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC sun bayyana sayen kuri’a a matsayin laifin cin hanci.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.