Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da shugaba Muhammadu Buhari a neman takara karo na biyu.
kwamishinan labarai da da al’adu na jihar kano, Malam Muhammed Garba ya bayyana hakan a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba cewa, Ganduje ya ce za a karfafa tsarin da gwamnati ke gudanarwa da ingantawa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawara ya sake bayar da ayyukansa ga kasar a 2019 .
Ya ce,”Buhari alama ce wanda a kowane bangare na kasar sun amince da shi a matsayin mutumin wanda za a iya dogara a kai”.
“Mu a jihar Kano misali, muna goyon bayansa dari bisa dari.
Mun san shi a matsayin dan Najeriya mai gaskiya wanda yake da kyakkyawar niyya ga kasar a kowane lokaci”.
Ayyukansa a cikin shekaru biyu da suka gabata musamman a yaki da cin hanci da rashawa, rashin tsaro da ta’addanci, abin misali ne.”
“Idan ya yanke shawara ya ji kukan mu don neman sake takara, za mu tallafa masa, kuma za mu yi duk iya kokarinmu kuma za mu tabbatar da cewa ya yi nasara azaben 2019”.Inji kwamishinan.
Su Kuma Jama,ar jahar kano bass bayanka domin basa kaunar gwamna ganduje.
Shin kuna tare da ganduje 2019
Souce In Mikiya
Add Comment