-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Zabar miji: Yadda wata amarya ta yi kuskure (2)


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga cikin yaran da suke yi wa Alhaji Balarabe aiki  akwai wani mai suna Abdullahi.  Abdullahi  ya shigo birni ne daga kauyensu don yin ci-rani. Yaro ne mai natsuwa da biyayya da iya zama da jama’a.  Hakan ya sa Alhaji Balarabe ya shaku da shi sosai, kuma ba a shago kadai ba, hatta dawainiyar gidansa Abdullahi ne yake yi.  Yakan aike shi don yin cefane ko zuwa banki don tura kudi ko kuma isar da sako a wuraren da Alhaji Balarabe ya tura shi.

An dauki lokaci mai tsawo Alhaji Balarabe bai taba samun wani sabani da Abdullahi ba.  Bai taba samun wani korafi daga gida ko shagonsa a kan Abdullahi ba.  Hasali ma Alhaji Balarabe ya sha gwada Abdullahi a lokuta da dama, don ya ga ko zai ci amanarsa, amma hakan bai faru ba.

Da Alhaji Balarabe ya fahimci Salma ta gama karatun jami’a sai ya yanke shawarar yi mata aure.  Sai dai kafin ya sanar da Salma sai da ya tuntubi Hajiya Maryam game da abin yake ransa na aurar da Salma ga Abdullahi.  Nan take Hajiya Maryam ta nuna hakan ba zai yiwu ba. “Ta yaya za a hada aure a tsakanin Salma da ta fito daga babban gida da kuma Abdullahi dan aikin gidansu?

Hakan ya ba Alhaji Balarabe mamaki da  takaici, inda ya nuna wa matarsa Maryam arziki fa nufin Allah ne.

Daga nan Hajiya Maryam ta hure wa Salma kunne kada ta kuskura ta yarda a aurar  da ita ga Abdullahi.

Alhaji Balarabe ya yi duk mai yiwuwa amma Salma ta kekasa kasa ta nuna ba ta son Abdullahi.  Da yake ba ya son ganin bacin ranta kuma gudun kada wani mummunan abu ya same ta, sai ya amince ta zabo irin mijin da take so.

Salma ba ta bata lokaci ba, ta sanar da saurayin da suke soyayya tun a jami’a, mai suna Mustapha cewa ya aiko a sanya musu ranar aure.

Nan da nan iyayen Mustapa suka gabatar da maganar aure, kuma aka sanya ranar aure, aka yi shagali da biki.

Da ma dukan gidajen biyu suna da dukiya, don haka ba a samu wata tangarba ba wajen gudanar da bikin a cikin kankanen lokaci.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 17

- Advertisement -

Salma da Mustapha suka tare a wani gida da mahaifin ango ya gina musu, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke, abin gwanin ban sha’awa.

Bayan wani lokaci, sai Salma ta samu juna biyu.  Tun daga lokacin ta rika yin laulayi, abin da ya sa ta rika kwanciya a asibiti a-kai-a-kai.

Akwai lokacin da Salma ta kwashe lokaci mai tsawo a asibiti saboda rashin lafiya.

Ashe Mustapa ba mutumin kirki ba ne. Sai ya yi amfani da damar wajen kai matan banza gidansa, hasalim a a gadon aurensu yake lalata da irin wadannan matan banza.

Ya shafe kwanaki bai leka asibitin ba, abin da ya daure wa Salma kai da kuma tunanin me ya faru? Ta san angonta Mustapha yakan kirata a waya sau da dama idan bai samu zuwa asibiti ba, amma yanzu ta shafe akalla kwana bakwai ba ta ji duriyarsa ba.

A takaice dai, an sallami Salma daga asibiti ba tare da sanin Mustapha ba.

Mu kwana nan

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: