Zababben Gwamnan Jihar kano Mai jiran Rantsuwa Engr. Abba kabir Yusuf ya Bayyana Kadarorinsa.
Engr Abba kabir yusuf da zaa rantsar Ranar Litinin mai zuwa a matsayin Gwamnan Jihar kano ya cike form din Bayyana kadarori kamar yadda dokar humar Kula da Da’ar Maaikata (CCB) ta tanada.
Daraktan Hukumar ta Jihar kano Hajiya Hadiza Larai ibrahim ce ta Marabceshi a ofishin hukumar inda ta bayyana Wannan abinda yayi a matsayin wani danba na nuni da cewa Gwamnatinsa zata kasance Gwamnatin Adalci da kuma yin abubuwa abisa doran doka.
A nasa bangaren Abba Gida Gida yace ya cika Tanadin kundin tsarin mulki. Kuma ya shaidawanhukumar cewa yanzu lokaci ne na Aikin Alumma.
Engr. Abba kabir yusuf ya jaddaa cewa duk wanda zaiyi aiki a karkashinsa dole ne shima ya dauki wannan mataki na Bayyana kadarori domin gudanar da Gwamnati mai Nagarta da kima a idon Alumma.
Add Comment