Kasuwanci

Zaa Gina Katafariyar Cibiyar Kasuwanci A Kano

– Gwamnatin jihar Kano za ta gina wata gaggarumin cibiyar kasuwanci mafi girma a yankin arewa a Kano

– Za a gina cibiyar a Dangwauro da ke a kan hanyar Zaria da hadin gwiwar kamfanin Brain & Hammers

– Gwamna Ganduje ya ce idan aka kammala cibiyar, zai samar wa matasa miliyan daya ayyukan yi

 

Aikin gina cibiyar kasuwanci wato Kano Economic City (KEC) wanda gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Ganduje tare da haɗin gwiwar kamfanin Brain & Hammers ke ginawa yanzu a garin Dangwauro da ke a kan hanyar Zaria ta yi nisa.

Kamar yadda Arewablog ke da labari, wannan cibiyar kasuwanci na daya daga cikin shirin gwamna Ganduje wanda bayan kammalawa zai taimaka da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Kano ta hanyar kawo kai tsaye masu zuba jari daga nan gida har kasashen waje.

A cewar gwamnan cibiyan kasuwancin (KEC) zai kuma taimaka wajen samar wa matasan jihar fiye da miliyan daya ayyukan yi. Idan aka kammala cibiyar zai kasance ya fi kasuwar Wuse da Asokoro da ke birnin Abuja girma.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement