Daga Comrade M.K Soron Dinki
Lallai an buga za6e a jihar Kano tsakanin APC da PDP. Tsohuwar jam’iya mai mulki tana so ta qwace mulki a hannun jam’iyar APC mai mulki a hannu. Har zuwa yanzu babu wata cikakkiyar hujjar yanke hukunci a za6en, sai a nan gaba muke sa ran jin sakamako insha Allah, duk da cewa an ga matasan kwankwasiyya suna ta boris da ababan hawa akan titi don bayyana farin cikinsu ga nasarar ‘dan takararsu.
- Advertisement -
Tabbas har zuwa yanzu babu wata karamar hukuma da aka bayyana alqaluman za6enta saidai sakamakon ‘yan “Social media” da yake yawo a facebook da WhatsApp da sauransu. A zaben dai an samu zaman lafiya kwarai da gaske saidai fatan Allah yasa a gama lafiya ya kuma za6a mafi alheri.