-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Za Mu Yaki Kungiyar IS’ -Al-Shabaab


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya ta ce za ta yaki kungiyar IS da ke cikin kasar.

Kakakin kungiyar Sheikh Ali Rage ne ya bayyana haka a cikin wata hira da ya fitar, inda ya yi kira ga mayakan kungiyar al-Shabaab su kai hare-hare ‘har sai sun shafe mayakan IS daga kasar’.

Duk da yake bangarorin biyu sun sha gwabza fada a wasu sassa na Somaliya a watannin baya bayan nan, wannan ne karo na farko da al-Shabaab ta fitar da irin wannan jawabin.

Kakakin kungiyar al-Shabaab ya saki sako na sautin muryarsa mai tsawon minti 42 a shafukan kungiyar na sada zumunta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

- Advertisement -

Kakakin kungiyar Sheikh Ali Rage ya zargi kungiyar IS da “kawo cikas ga yakin jihadin da ake yi a Somaliya”.

Ya kuma kira kungiyar ta IS a matsayin “wata muguwar cuta” kuma “cutar daji”, kuma ya kira mayakan al-Shabaab da su yaki kungiyar ta IS a kasar.

Da alama wadannan kalaman na mayar da martani ne ga ikirarin da IS ta yi cewa mayakanta sun kashe wasu mayakan al Shabaab a yankin Puntland.

Kungiyoyin biyu sun sha gwabza fada tun bayan da IS ta bayyana a Somaliya, inda ta kafa sansanoninta a arewacin kasar, kuma ta fara karbar kudin kariya daga ‘yan kasuwan kasar, kamar yadda rahotanni daga kafafen watsa labarai suka ruwaito

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: