Za Mu Kwashi Matafiya Kyauta A Duk Ranar Da Buhari Ya Dawo Gida Nijeriya, Cewar Kungiyar Darebobin NARTO Reshen Jihar Jigawa
Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori
Kungiyar Derebobi ta NARTO reshen jihar Jigawa ta ce za ta yi jigilar matafiya kyauta a dukkan kananan hukumomin jihar Jigawa zuwa Birnin Dutse a duk ranar da Allah ya dawo da shugaban kasa Muhammadu Buhari gida Nijeriya lafiya.
Shugaban kungiya na kasa shiyyar Hadeja, Alhaji Muhammad Zalanga ne ya baiyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake bayyana farin cikinsa dangane da rabon sabbin motoci da gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ta yi wa Kungiyar a matsayin bashi mara kudin ruwa, domin saukaka sufiri a fadin jihar da ma sassan Nijeriya.
Daga karshe shugaban kungiyar ya umarci dukkanin ‘ya’yan kungiyar da su rinka sanya shugaba Buhari a cikin addu’oinsu domin Allah ya ba shi lafiya.
Add Comment