Labarai

Za mu farfado da bankin Arewa – Gwamnonin Arewa

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce gwamnonin arewa 19 sun fara tara kudaden da za su bukata wajen sake farfado da bankin Arewa wato Bank of the North.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake tattaunawa da yan majalisar zartaswa na jihar Kano inda ya ce gwamnonin sun amince suyi haka ne a taro da suka yi a Kaduna.

Ganduje ya kara da cewa gwamnonin sun yarda su farfado da wasu manyan masana’antun da suka durkushe a yankin arewacin Najeriya musamman masa’antun masaka.

 

Ya ce sauran abubuwan da suka tattauna a zaman sun hada da samar da zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya da kuma warware rikicin Fulani makiyaya da manoma.

Daga karshe Ganduje ya sa hannu akan wasu dokokin da aka gyara wanda ya hada da dokar jami’ar kimiya da fasaha na jihar Kano da na jami’ar arewa maso yamma.

Tags