Labarai

Za Mu Damka Wa Gwamnatin Kaduna Al-Zakzaky-Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta kamala duk wani shirye-shirye na mika Sheikh Ibrahim Zakzaky ga gwamnatin jihar Kaduna bisa jagorancin Malam Nasir El-Rufa’i domin ci gaba da sauraron kararraki akan Zakzakin
Wannan ya biyo bayan rattaba hannu akan takardun tabbatar da wannan izini da ministan shari’a, Malami Abubakar ya yi 
Kafin wannan izini dai gwamnatin jihar Kaduna bisa jagorancin Malam Nasir El-Rufa’i ta nemi da gwamnatin tarayya ta danka Zakzaky a hannuta sa’annan ta riqe wani dan darikar Shi’a na daban a maimaikon Zakzakyn, amma sai a wannan lokaci ne gwamnatin tarayya ta bayar da wannan izini
Bukatar ta gwamnatin jihar Kaduna na damka mata Zakzaky don ta shigar da shi kara a kotu bisa laifukan da ya aikata na kusan shekaru 30 ya ci karo da hukuncin da wata babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta yanke na a saki Zakzakyn tare Kuma da gina masa gida daya daga cikin jihohin arewacin Nijeriya
A farkon wannan makon ne dai IMN ta sanar da halin yanayin gurbacewar lafiya da Zakzakyn ya shiga a hannun hukumomin Nijeriya.