ZA A KADDAMAR DA KAMFANIN SHINKAFA A JIHAR KEBBI
Daga Yahuza Sahabi Dandede Kamba
Shirye-shirye sun kan kama, inda jami’an tsaro na ta sintiri a wuraren da za a yi taron bude kamfanin casar shinkafa a garin Argungu dake jihar Kebbi.
Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ne zai jagoranci bude kamfani shinkafa wato (WACOT RICE LIMITED).
Yanzu haka gwamnoni da suka hada da gwamnan Jigawa da Imo da na Adamawa dadai sauransu duk sun sauka jihar ta Kebbi don halartar wannan buki kuma gwamnan na jihar Kebbi shine mai masaukin baki.
Add Comment