Kocin Everton Ronald Koeman ya yi matukar takaicin tuhumar da ake wa Wayne Rooney da yin tuki cikin maye, inda ya ce za a dauki mataki a kan dan wasan a cikin gida.
A ranar Juma’a ne aka kama Rooney, bayan da ‘yan sanda suka tsayar da motarsa kirar VW Beetle a Wilmslow.
Sai dai an bayar da belin tsohon kyaftin din Ingilan, inda daga bisani kuma zai bayyana a gaban kotun Majistrin birnin Stockport nan gaba a cikin watan nan.
A ranar 18 ga wannan watan ne kotu za ta saurari karar, washe garin ranar da Everton za ta je Manchester United don ci gaba da gasar Premier.
Wasan shi ne zai zamo na farko da Rooney zai buga a Old Trafford tun bayan barinsa Manchester United inda ya koma Everton.
Koeman ya ce, “Mun tattauna ranar Talata , kuma Bill Kenwright ya yi magana da shi game da halin da yake ciki”.
Ya kara da cewa, “Za mu dauki matakin da ya dace da shi a cikin gida kuma a lokacin da ya dace”.
Add Comment