Labarai

Za a halatta kananan matatun mai a Naija Delta

Mukaddashin shugaban kasa ne ya gana da shugabannin Naija Delta kan lamarin

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta halatta kananan matatun mai a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur, tare sayar musu da danyen mai a farashi mai rahusa a karshen shekarar nan.

Matakin na nufin kawo karshen satar danyen man da ake yi daga bututan mai a yankin, wanda ke da haramtattun matatun mai da dama da suke sarrafa man da ake sacewa.

Mazauna yankin na kukan ba sa cin gajiya daga albarkatun man fetur din a yankin nasu.

 

An bayyana shirin ne bayan wata ganawa da tsakanin mukaddashin shugaba Najeriyar Farfesa Yemi Osinbajo da shugabannin yankin.

Ofishin shugaban kasar ya kuma ce zai tattauna da kamfanonin hakar man masu hedikwata yankin na Naija Delta.

Ko wacce jiha da ke yankin Naijka Delta za ta samu kananan matatun mai biyu da za su fara aiki a watanni uku na karshen wannan shekarar.

Shugabannin yankin sun ce sun yi farin ciki da wannan mataki da gwamnati ta dauka.

Masu ta da kayar baya na yawan fasa bututan mai a Naija DeltaMasu ta da kayar baya na yawan fasa bututan mai a Naija Delta

Tun a shekarar da ta gabata gwamnati ke ta ganawa da shugabannin al’ummomin yankin Naija Deltadon kawo karshen hare-haren da ake kai wa kan manyan bututan mai mallamar gwamnati da kamfanonin mai.

Sai dai masu tayar da kayar baya na yankin sun ci gaba da barnar da abin da ya jawowa Najeriya asarar miliyoyin daloli, kuma masana tattalin arziki suka ce hakan ya taimaka wajen durkushewar da tattalin arzikin kasar a bara.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.