Mai Shirya fim din, Ali Sa’id ya ce a wata mai zuwa ne za a fara fim mai dogon zango mai taken “Hanifa” kan yarinyar da aka kashe a Kano.
Ali Sa’id ya ce babban dalilinsu na yin fim din shi ne domin wayar da kan iyaye kan yadda za su saka ido kan yaransu bayan abin da ya faru da Hanifa.
“Muna kuma son a rika tunawa da Hanifa ta hanyar wannan fim din” a cewar mai shirya fim din.
Iyaye da dama sun nuna sha’awar wannan fim din kuma sun kawo yaransu domin fitowa a matsayin Hanifa a fim din.
Ga Masu So Shiga Wannan Fim din sai Su kira wannan lambar: 08030595938
Add Comment