Kannywood

Za a yi wa harkar shirya fina-finai garanbawul

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce za ana so harkar fina-finai ta habaka a Najeriya

Ministan yada labarai na Nigeria Alhaji Lai Mohammed, ya kaddamar da wani kwamiti na majalisar shirya fina-finai na kasar MOPICON a ranar Talata.

Ya kaddamar da kwamitin ne a wani kokari na ganin an gabatar da kudurin doka na MOPICON da gaggawa.
Da yake kaddamar da kwamitin a birnin Lagos, Alhaji Mohammed ya karyata jita-jitar cewa gwamnati ta samar da hukumar ne domin samun damar sarrafata yadda ta so.
Ministan ya ce kokarin gwamnati shi ne domin bai wa fagen shirya fina-finai na Najeriya damar taka rawarsu wajen cigaban kasa.
Ya kara da cewa hakkin ma’aikatarsa ne ta sa ido kan harkar fina-finai da kuma yadda za a tallafawa bangaren.
A karshe ya bai wa kwamitin wanda ya hada da wakilan kungiyoyi daban-daban da hukumar tace fina-finai ta kasa makonni uku su kammala aikin da ya basu tare da mika masa rahoto.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.