Labarai

Za A Sake Buɗe Dukkan Makarantun Kwana Ta Mata A Jihar Katsina

Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe duka makarantun kwana na mata a faɗin jihar, domin ƙarasa zangon karatu na shekarar 2020/2021 daga ranar Lahadi 28 ga watan Maris.

Haka kuma gwamnatin ta ba da umarnin a buɗe wasu makarantun kwana guda biyar a jihar.

An ba da umarnin ‘yan mata su koma makarantu jeka ka dawo da ke kusa da su a ranar Laraba 24 ga watan Maris.

Ga Jerin makarantun da aka bada umurnin budewa; makarantar sakandiren gwamnati dake Malumfashi (Unity), SUNCAIS Katsina, Makarantar mata ta gwamnati dake Dutsin-Tsafe, makarantar sakandiren mata Dutsinma, makarantar kurame dake Malumfashi, da kuma makarantar makafi Katsina.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: