Labarai

Za A Maka Dan Fim Din Da Ke Batawa Musulunci Suna A Kotu

Wani mai rajin kare addinin musulunci mai suna Lawal Muhammad Gusau, ya gargadi jarumin Barkwanci CHINEDU ANI EMMANUEL da ke garin Legas da ya daina aikace-aikacen Barkwanci da Rigar Musulunci.

A wata budaddiyar wasika da Gusau ya aikewa Emmanuel, ya ja kunnen sa, tare da gargadin sa da ya daina irin wannan kyakkyawar shiga irinta musulunci (Sanye da jallabiya da Ghutra) yana fakewa da cewa shi cikakken musulmi ne, yana fitar da bidiyoyin da basu dace ba.

Gusau ya kara da cewa, bisa la’akari da abubuwan da muke gani a shafinka nal YouTube channel mai suna (Official Nedu Tv) muna sake jan kunnen ka, da ka daina yada irin abubuwan da ka ke yadawa na nunawa Duniya cewa Bahaushe fasike ne, jahili ne, wanda bai da aikin yi.

Ba tare da wani kokonto ba, tuni mun riga mun umarci lauyoyin mu, da manyan hukomomin shari’a da su ci gaba da bin kadin wannan korafi, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba, har sai mun tabbatar da ka fito karara ka nemi afuwar da kuma gafarar musulman Duniya, saboda addinin musulunci addini ne na zaman lafiya.

An dade dai ana korafi game da bidiyoyin jarumin, inda wasu ganin ya wuce gona da iri, kuma kullum kara fadada su kawai yake.

Emmanuel yana fitowa da sunan Malam Musa, a wasu shirye-shiryen Barkwanci da ya ke yi a yanar gizo, sannanma’ikaci ne, a gidan Rediyon Wazobiya FM da ke Lagos, kuma ya kan fito a wasu Finafinan kudancin kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: