Marigayiya Hauwa Ali Dodo na daya daga cikin wadanda za a karrama a bikin raba kyautuka na AMMA Awards na wannan shekara.
AMAA Awards shi ne bikin karrama mawaka da masu shirya fina-finai na Arewa, kuma marigayiya Hauwa Ali Dodo na daya daga cikin tsoffin jaruman Kannywood.
Abubakar Sabo Usman daya daga cikin jami’an shirya bikin ya ce, za’a karrama marigayi Tijjani Ibrahim da kuma wasu tsoffin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai da wakokin Hausa da kuma wadanda suka bayar da gudunmawa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood wacce ta cika shekaru 25 da kafuwa.
AMMA Awards na daya daga cikin bukukuwan da ake gudanarwa domin karrama wadanda suka bayar da gudunmawa a fagen fina-finan Hausa, za kuma a gudanar da bikin ne a ranar Asabar a jihar Kano, Najeriya.
Add Comment