Labarai

Za A Kai Abduljabbar Gidan Mahaukata

A cewar Alƙali Ibrahim Sarki Yola,”hujjar da lauyoyin Abduljabbar sukayi na Sukar cewa ba’a sake gabatar da chaji da farko a gaban kotun musulunci sannan a kawo wani sabon chaji, Alƙali Sarki Yola yace Lauyoyin Abduljabbar basu fahimci abin ba, inda ya kafa hujja da cewar babar kotun tarayya tace Takardar tuhuma ta Yansanda FIR ba takardar tuhuma bace”.

Saboda wadannan dalilai kotu ta amince da a karanatawa wanda ake kara sabbin tuhume tuhumen da ake masa, ya musanta ko ya amince da su.

Sai dai lauyoyin Abduljabbar sun yi suka kan haka inda suka ce basu amince da hakan, Wanda in aka ci gaba da haka zasu daukaka kara.

Alƙali Sarki Ibrahim Yola yace dole ne a karantawa Abduljabbar Nasir Kabara Sabon chajin da ake masa.

Barista Shuaibau Sa’idu SAN ne ya karanto Chajin kamar haka:

“Ranar 10/8/2018 Abduljabbar a unguwar Sani Mai nagge a karatun ka na Jauful Fara inda ka yi wa Annabi SAW qage na cewar a hadisi na 1365 da na 1358 na sahih Muslim cewa (Annabi SAW fayde yayi wa Nan Aisha), wanda hakan ya sabawa sashe na 382 (b) kundin tsarin shari’ar mausulunci ta 2000”

Kotu ta tambayi Sheikh Abdujabbar kan tuhumar da aka yi masa, shin ya fadi hakan, amma Abduljabbar yayi shiru bai ce komai ba.

Tuhuma ta biyu:

”Ranar 10 ga watan 8, 2018, a karatun ka na Jauful fara kayi amfani da kalaman batanci ga Annabi inda kayi masa kage kan auren sa da Ummu Safiya, Kace Muslim yace Annabi ya kwacewa wani mutum matarsa a hadisi mai lamba 1365, wanda hakan cin zarafi ne, laifi me da ya sabawa sashe na 382(b)”

An sake tambayar Sheikh Abduljabbar ko ya fahimci abin da ake tuhumar sa, amma yayi shiru bai ce komai ba.

Tuhuma ta uku:

” a ranar 10/08/2019: a karatun Jauful fara darasi na 40 kayi amfani da kalaman batanci cewar matar Annabi, Saffiya dole yayi mata ya aureta, in tana san yancinta, Wanda babu wannan hadisi kai ka kirkire shi, kuma hakan ya sabawa sashe na 382 (b) na kudin tsarin Shari’ar Musulunci na Kano na 2000”

Anan ma an sake tambayar Sheikh Abduljabbar Kabara akan ko ya aikata, amma yayi shiru bai ce komai ba.

Tuhuma ta huɗu:

”a darasi na 90 da na 98 na karatun sa na Juful fara ya kagawa Annabi laifin zina, inda yace wata mata tanemi annabi ya biya mata bukatar ta, inda yace take zai zo ya biya mata bukata kuma yayi hakan, wanda ya saba da sashe na 382 na kundin hukunta laifufuka na shariar Musulunci na 2000 ta jihar Kano.

Alkali Sarki Yola ya sake tambayar Abduljabbar kamar farko amma yayi shiru kamar dai yadda aka yi masa a farko.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: