KannywoodLabarai

Za a hana ɗora fina-finan Kannywood da ba a tantance ba a Youtube

Wata sanarwa da Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa wato National Film and Video Censors Board ta ja kunnen furodusoshin Kannywood kan fitar da fina-finai da waƙoƙi da suke yi a shafin Youtube ba tare da hukumar ta tantance su ba.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Umar G. Fage, muƙaddashin babban jami’in da ke kula da shiyyar arewa maso yammacin Najeriya a hukumar ta ce, haƙƙin hukumar ne ta bai wa duk wani mai shirya fim lasisin fitar da ko wane irin bidiyo.

Umar G. Fage ya shaida wa mane ma labarai  cewa masu shirya fina-finan sun saɓa wa sashe na 5 (1), 33 (1) na dokar hukumar ta 1993, cap. N40 LFN 2004 da kuma Dokar 2008.

“Don haka duk wanda ya saki fim ko bidiyo a shafin Youtube ya yi laifi kuma yana iya fuskantar hukunci saboda dokar ta ce ne a ko ta wani nau’i mutum zai fitar da fim dole ne hukuma ta tantace” a cewarsa.

A baya-bayan nan dai furodusoshi da dama sun tattare a shafin Youtube inda a nan ne suke fitar da fina-finansu saɓanin yadda aka sani a baya da ake fitar da fim a kan faifan CD.

Kuma ana iya alaƙanta haka da matsalar satar fasaha da suka daɗe suna fama da ita, inda wasu ke ɗaukar fina-finai su buga marasa inganci sannan su sayar a farashi mai arha.

Sai dai shahararren mai shirya fina-finan nan Falalu Ɗorayi ya ce a nasa ɓangaren ba ya ja da batun tantance fina-finai kafin a sa a Youtube.

“Ya yi dai-dai a riƙa tace ko wane fim ko waƙa kafin a fitar, dama haka ya fi dacewa,” in ji Falalu.

Sai dai ya ce ya kamata hukumar ta NFVCB ta fahimci cewa ba wani kuɗi masu shirya fina-finai ke samu ba a Youtube kafin ta bijiro da wani hukunci a kansu.

“Duka-duka kuɗin da muke samu a Youtube bai yi rabi-rabin abin da muke samu a baya ba lokacin da muke yin fim a kan CD. Don haka ɓullo da wannan mataki da hukumar ta yi ba shi da wani amfani idan ba za ta taimaka mana da kasuwancin fim ba,” a cewarsa.

Ya ce duka hukumomin da ke sa ido kan harkar fim ba su yi wa furodusoshi wani abun a zo a gani ba kuma a matsayinsa na mai shirya fim ba shi da wani buri illa ya ga harkar kasuwancin fim ta bunƙasa.

“Ba don wani abun muke ɗora fina-finai a Youtube ba, kawai dai don kara a yi ba mu ne. Kuma kana nishaɗantar da masu bibiyarka,” a cewar Falalu Ɗorayi.

Umar G. Fage na hukumar NFVCB ya bayyana cewa suna nan suna tattaunawa da kamfanin Google mai shafin Youtube don ganin an yi maganin masu dora fina-finai da waƙoƙin a Youtube ba tare da an tantance su ba.

“Muna nan muna tattaunawa da Google kan yadda za mu hana ɗora waɗannan finan-finan da waƙoƙi da ba a tantance ba. Hatta na baya da aka riga aka ɗora ba tare da tantancewa ba, su ma za mu san yadda za a yi” in ji shi.

Ba wannan ne karon farko da hukumomin da ke sa ido kan harkar fina-finai suka samu matsala da furodusoshi ba.

Ko a kwanakin baya ma sai da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayar da umarnin a daina sakin fina-finai da waƙoƙi a Youtube ba tare da ta tantance su ba.

Sulaiman Lawan

Sulaiman Lawan Usman is a graduate in Bsc Mechanical engineering from Kano University of Science and Technology, Wudil. Also a founding member of ArewaBlog. And now he is working with Vision FM Nigeria as Head of engineering

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: