Labarai

Za A Fara Rataye Masu Garkuwa Da Mutane Da ‘Yan Bindiga A Jihar Neja

Daga Comr Abba Sani Pantami
Majalisar dokokin jihar Neja ta yi sabuwar doka wacce ta bada umurnin a rika yanke wa duk wanda aka tabbatarwa laifin garkuwa da mutane ko dan bindiga hukuncin kisa ta hanyar rataya.

News Wire ta ruwaito cewa ‘yan majalisar sun kuma ce dokar za ta yi aiki a kan duk wanda aka samu yana hada baki ko taimakawa yan bindiga da masu garkuwa a jihar.

Majalisar dokokin jihar yayin zamanta na ranar Talata ta amince da kudin yi wa dokar hana garkuwa da mutane da satar shanu ta shekarar 2021 kwaskwarima.

Kungiyoyin bata gari sun kasance suna kai hare-hare a sassan jihar har ma da makarantu inda babu cikakken tsaro sannan su sace dalibai su tafi da su daji domin neman a biya su kudin fansa.

Idan za a iya tunawa, a watan Mayun wannan shekarar yan bindigan sun afka garin Tegine a jihar Niger inda suka sace dalibai a wata makarantar Islamiyya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: