Labarai

Yunwa Na Yunƙurin Hallaka Ƴan Gudun Hijira A Jihar Katsina

Yunwa Na Yunƙurin Hallaka Ƴan Gudun Hijira A Jihar Katsina

 

A wasu bayanai da “Katsina Reporters ta samu na bayyana cewa yunwa na ƙoƙarin hallaka ƴan gudun hijira sakamakon rashin wadataccen abinci a sansanonin ƴan gudun hijirar na jihar Katsina.

 

A wani rahoto da muka samu yan gudun Hijirar suna cikin wani mawuyacin hali na ƙuncin rayuwa da matsananciyar yunwa a wasu sansanin ƴan gudun hijirar daban da aka keɓance mutane a fadin jihar.

 

A wani bangaren Kuma ƴan gudun hijirar suna samun tallafi daga wajen mutanen gari, kama daga omo wanki da sabulun wanka da kayayyakin abinci da dai sauransu.

 

Mafi yawancin mutanen da suke rayuwa a yawancin sansanin ƴan gudun hijirar mutane ne waɗanda su yi ƙaura ne daga garuruwansu a dalilin matsalolin da ya jefa al’umma cikin zullumi.