-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yunkurin Tsige Buhari: Bukola Saraki Ne Ya Ingiza Ni, Inji Sanata Mattew Oroghide


0 441

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

YUNKURIN TSIGE BUHARI:

Bukola Saraki Ne Ya Ingiza Ni, Inji Sanata Mattew Oroghide

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya ingiza ni wurin gabatar da kudurin neman a tsige shugaban kasa saboda mu sanyawa gwamnati tsoro don ta dakatar da tuhumce-tuhumce da ake yiwa sanatoci.

Sanin kowa ne cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa yana fuskantar tuhuma yanzu haka, akwai Sanata daga jihar delta da yake gidan yari, Ga kuma Dino Melaye da yake fuskantar kiranye daga mazaɓarsa.

“Na ji matukar mamakin yadda senetoci ƴan uwanmu suka juya mana baya ni da wanda ya mara mini baya yayin gabatar da kudirin na neman tsige shugaban kasa”.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

“A gaskiya abokan aikinmu sunci amanar mu sakamakon sanyamu gaba wurin faɗa da fadar shugaban kasa.”

“Gwamnar jiha ta yana fushi dani ya daina ɗaukar wayata, ina fuskantar barazana daga al’ummar mazaɓata, toh a gaskiya wannan al’amari ya tayar min da hankali kuma ya jefa ni cikin shakku.”

“Saboda haka kada ku zarge ni, shugaban majalisar dattawa ne yafi dacewa da ku zarga saboda shi ne silar wannan batu”.

“Gaskiyar magana shi ne ban isa in fuskanci fadar shugaban kasa da irin wannan batu ba.”

Ranar litinin dake tafe zan kira taron ƴan jarida don in bayyana musu matsayina akan haka.” Inji Sanata Mattew Oroghide

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.