Labarai

An Yi Wa Gidan Jonathan Dake Abuja Kar-karf

An Yi Wa Gidan Jonathan Dake Abuja Kar-karf

…ana zargin ‘yan sandan dake gadin gidan da kwashe kayan

…an kama ‘yan sanda uku da ake zargi

An yi wa gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan dake Abuja kar-kaf.

Saidai rahotanni sun nuna cewa akwai alamar ba barayi ne suka shiga gidan ba, wanda hakan ya sa ake zargin ‘yan sandan dake gadin gidan da kwashe kayan.

Majiyarmu ta rawaito cewa tuni rundunar ‘yan sanda ta kama jami’anta guda uku da ake zargi da sace kayayyakin na kimanin milyoyin kudade dake cikin gidan mai lamba 89 dake Fourth Avanue Gwarimpa Abuja.

 

Wasu kayyakin da aka kwashe a gidan sun hada da;

1. Kaya dinkin yankin Niger Delta cike a cikin jaka Ghana-must-go guda 20.

2. Riga kirar kwat cikin Ghana-must-go guda biyar

3. Kayan mata da aka yi wa dinkin yankin Niger Delta makare cikin manyan jakunkunan Ghana-must-go guda goma

4. Atamfofi guda goma.

5. Setin babbar riga guda goma.

6. Babbar jaka ta Ghana-must-go mai dauke da kaya masu dauke da logon jam’iyyar PDP

7. Hulunan malafa guda 20.

Kayan wuta da na daki da aka sace

1. Talabijin kirar Plasma guda 36 .

2. Firiza guda 25.

3. Setin kayan daki guda biyar.

4. Manyan kujerun falo guda biyu.

5. Na’aurarorin sanyaya daki.

 

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.