-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yemi Osinbajo Ya Sha Kaye A Rumfarsa


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jam’iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Kazalika jam’iyyar ta PDP ta yi nasara a rumfar zaben dan takarar gwamnan Lagos na jam’iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu.

Dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya samu yawan kuri’u 384, a rumfar dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam’iyyar APC a Lagos.

Osinbajo da ke takara da shugaba Buhari a jam’iyyar APC, sun samu yawan kuri’u ne 197

Mataimakin shugaban kasar ya sha kaye ne duk da ya bi layi tare da jama’a domin kada kuri’arsa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

- Advertisement -

Tun da safe Osinbajo ya kada kuri’arsa a rumfarsa da ke Victoria Garden City a Lagos.

A akwatu mai lamba Ward 019 da ke mazabar Lateef Jakande/Femi Okunnu a unguwar Ikoyi inda Sanwo-Olu ya kada kuri’a, PDP ta samu 52, yayin da APC ta samu 48.

Mutane dai za su yi mamakin yadda mataimakin shugaban kasar ya gaza lashe rumfarsa ganin yadda ya bi gida-gida sako da lungu a yankin kudu maso yammaci yana yakin neman zabe.

Kazalika za su yi mamakin shan kayen da Sanwo-Olu ya yi a akwatunsa, ganin cewa shi ne dan takarar gwamnan Lagos a APC mai mulkin jihar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: