Kiwon lafiya

Yaya ‘yan siyasa ke fama da karancin bacci?

Ba kasafai ‘yan siyasa ke samun wadataccen bacci ba. To ta yaya su ke aiki da dan hutun da bai kai ya kawo ba?

Michael S Jaffee na jami’ar Florida ya yi mana nazari.

Bukatar zama shugaban kasa na dauke wa mutane damar yin bacci sosai, kuma idan ma mutum ya yi nasarar zama shugaban babu abin da zai ragu, sai dai ma rashin baccin ya karu.

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya tsarawa kan sa bacci na sa’o’i shida a duk dare, to sai dai ba kullum hakan ke samuwa ba.

rashin bacciHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

To wai shin baccin sa’o’i nawa ya kamata shugabannin mu su rinka yi idan har ana so su yi aiki yadda ya kamata?

Wannan tambaya ce mai muhimmanci ga duk wani dan siyasa da ya daura damarar yakin neman zabe. Shin bacci yana shafar yadda suke gudanar da al’amuransu?

Ya ma suke tsara lokutan baccin na su? Shin rashin isasshen bacci na daga abubuwan da suke sa su rinka yin kusukure a cikin jama’a?

TrumpHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

A matsayi na na likitan kwakwalwa, wanda ya yi nazari kan bacci tsawon shekaru da dama, na san cewa bacci na shafar yadda muke gudanar da al’amura da kuma lafiyarmu.

Baccin sa’o’i hudu ko biyar yana isar wasu, wasu kuwa suna bukatar yi fiye da haka.

Har yanzu masu bincike na kimiyya sun kasa gano dalilin da ya sa muke bacci, da kuma irin amfanin sa, to sai dai bincike ya nuna cewa bacci ya na da alfanu masu yawa ga lafiyar mu da jikin mu da kuma kwakwalwar mu.

Wani sakamakon bincike na hadin gwiwa da cibiyar nazarin bacci ta Amurka da kuma kungiyar masu bincike kan al’amuran bacci suka wallafa a bara ya bada shawarar cewa, ya kamata cikakken mutum ya rinka samun baccin sa’o’i bakwai a kowane dare in har yana so ya kiyaye lafiyar sa.

Sun kara da cewa yin bacci na kasa da sa’o’i bakawai a kai- a kai bai isa ba, kuma zai iya janyo illa ga lafiya.

Akwai dai shedu da aka samu shekaru da dama da suke nuna amfanin bacci, wajen rage cutukan da suke kama dan adam idan shekarun sa sun fara nisa, musamman ma cutukan mantuwa da kuma wadanda su ka shafi kwakwalwa.

Sassan Kwakwalwarmu na musayar bayanai da juna a lokacin da muke bacci, wanda nan kuma matattara ce da ke aika duk wasu bayani zuwa sassan jiki.

Bincike kan dabbobi ya nuna cewa bacci na bada damar wanke kwakwalwa daga wasu tarkace da ba ta bukatar su, wadanda idan suka taru su ke haifar wa mutum matsala ta tabin kwalkwalwa.

Rashin bacciHakkin mallakar hotoSCIENCE PHOTO LIBRARY

Akwai bincike da dama da suka nuna raguwar irin ayyukan da kwakwalwa ke yi sakamakon karancin bacci.

Ayyukan sun hada da fadaka, da daidaita irin martanin da ya kamata mutum ya mayar idan wani abu ya faru da shi, da koyar abubuwa da kuma hadda, sannan da “jagoranci”.

Bincike ya nuna cewa jagoranci shi ne iya tunkarar abubuwa da dama, sannan da tsara abubuwa masu rikitarwa, bugu da kari da iya mallakar kai, da tace halayen da ya kamata a nuna, da kuma zabar kalmomi da ya kamata a yi amfani da su yayin magana, don kaucewa subul-da-baka.

Akwai kuma bincike da dama da suka nuna ana yawan samun kura-kurai da karuwar hadura yayin tuki idan aka samu karancin bacci.

Haka kuma akwai tasiri da dama na illar rashin bacci da aka gano, da suka hada da karin kiba, da tara teba, da ciwon suga, da hawan jini, da matsalar damuwa, da kuma hadarin kamuwa da ciwon zuciya, har ma da mutuwa.

Rashin bacciHakkin mallakar hotoSCIENCE PHOTO LIBRARY

Bayan an gano cewa rashin bacci yana yawan haifar da kuskure da hadari yayin tuki, akwai kuma wasu binciken da suka gano cewa masu shekaru da yawa da ke wasan motsa jiki suna kara samun kuzari ta hanyar kara lokutan baccin su da daddare.

Ta ya za ka magance mastalar rashin bacci?

Shan abubuwan da ke hana bacci: Akwai wasu sinadarai da ke taruwa a bangaren gaba na kwakwalwar mu da ake kira adenosine a turance, wadanda su ne ke sa mu ringa jin bacci.

To an gano cewa shan abubuwan da ke hana bacci kamar cofee da cin goro na hana wadannan sinadaren aiki na dan wani lokaci.

Gyangyadi: Akwai shedu da ke nuna cewa gyangyadi (da bai wuce minti ashirin ba) zai dan wartsakar da mutum, ya sa ya dawo hayyacin sa.

Kuma hakan ya zama wata al’ada ta masu mulki, inda suke amfani da gyangyadi dan ragewa kan su tarin bacci, su kuma dan sarara.

Samun wani waje mai nutsuwa a wajen aiki da za a iya dan runtsawa abu ne mai taimakawa.

Amfani da na’urorin farkarwa: Dogaro da na’urori wajen farkar da mutum daga bacci na karuwa.

Ana amfani da agogo da wayoyin hannu dan taimakawa mutum ya tsara al’amuran sa ta yadda za su rinka tunatar da shi da kuma farkar da shi a lokacin da ya ke so.

A wasu lokutan ana kiran irin wadannan na’urori karamar kwakwalwa.

Shugaba ya kan samu wasu mutane da ke taimaka masa wajen tsara abubuwa da dama, da kuma taya shi gudanar da wasu abubuwa da suka zama dole, gami kuma da warware matsaloli a duk lokacin da suka taso.

Hakan dai ya nuna muhimmancin samun mataimaka masu yawa ( wadanda wasu ba su da matsalar bacci) da za su rinka taimakawa kwakwalwar shugaba.

Watakila irin wadannan mataimakan da shugabanni ke amfani da su su ne ke sa ba a ganin kasawar su duk kuwa da cewa ba sa samun isasshen bacci yadda ya kamata.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How do politicians get by on so little sleep?