Yaya Maza Su Ke Soyayya? (1)

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Idan so mu ke mu yi wa lamari kyakkyawar fahimta, sau da yawa asalinsa mu ke komawa. A haka ne mu ke iya gano ainishin inda ya samo suffa da dabi’a da dangoginsu. Annabin Allah Adamu (AS) ya kasance a cikin gidan aljanna, shi kadai, lokaci mai tsayi. Amma tare da cewa gidan aljanna gida ne wanda ya kunshi dukkan wani abu na more rayuwa da dan’adam ka iya bukata.

Wataran sai ya wayi gari ya kasa samun sukunin more abubuwan alfarmar da ke cikinta. Sukuni da walwalarsa su ka ragu. Ya fara ji a jikinsa cewa lallai akwai wani abu da ya rasa. Ba komai ya dame shi ba a wannan lokaci face wahasha da ya tsinci kansa a ciki. Wato halin kadaici, saboda shi kadai ne a cikin aljanna. Da Allah subhanahu wa ta’ala Ya yi nufin fitar da shi daga wannan yanayi, cikakkiyar fitarwa. Bai turo masa aboki ko da ba. Sai ya turo masa mace.

Talla

Ita ce uwarmu Hauwa’u, {RA}. Wadda zuwanta shi ne ya zama sanadin korewar damuwarsa (AS) Wannan tushen shi ne zai haskaka mana yadda rayuwar soyayyar maza har ma da matan takan kasance har zuwa yau. Amma fa idan har za mu iya yi masa karantu irin na ta nutsu. A bangare guda, masana dabi’un dan’adam suna kwatanta duniyar maza da cewa duniya ce da duk mutanen cikinta su ka shiga damuwa, a wani lokaci. Su ka koma cikin kogunnan duwatsu suka zauna ba tare da sanin me ne ainishin abin da yake damun su ba.

Har sai da labarin duniyar mata ya zo musu. Suka kuma yi tattaki su ka je har waccan duniyar. Inda a can ne suka sami cikakkiyar nutsuwa sakamakon zamansu a tare da juna. Kafin wannan haduwa, masana suna kwatanta tsarin rayuwar maza da cewa tsari ne na win/lose. Wato ni in samu kai ka rasa, ko kuma ni in ci nasara kai ka fadi. Wanda har yanzu wannan tsari yana nan a cikin wasu wasanni na mazan. Kamar a wasan “Table tennis” inda za ka ga mutum ba wai so yake kawai ya yi nasara ta hanyar dawo da kwallon da ka buga masa ba. A’a so yake wai kai ka kasa samun nasarar taro ta.

Don haka sai ya bugo maka da karfi ko kuma can wani gefe, dole sai dai ka fadi. Shi kuwa ba ruwansa, rashin nasararka ko a jikinsa, in dai shi ya yi nasara. A duniyar mazan, a tsakaninsu, wannan ba komai ba ne, tsari ne da aka amince da shi. Ko ba komai dai kai ma ka koyi jarumta, yadda za ka iya dogaro da kanka. Amma bayan haduwarsu da mata, sai suka fahimce lallai matan ba za su iya rayuwa a kan irin wancan tsari ba. Don haka dole tsarin ya sauya. Maza suka koma tsarin win/win.

Wato ni in yi nasara kai ma ka yi nasara. Wannan sauyi kuwa ya faru ne sakamakon yadda suffofi da dabi’un da al’adun mata suka bayyana ga maza. Ba su da karfin damtse da juriya da jarumta da rashin tsoro irin na maza. Don haka idan an tafi a kan wancan tsari su ba za su iya kaiwa gaci ba kenan. Sannan kuma idan sun kasa rayuwar mazan za su koma halin da suka tsinci kansu na damuwa da rashin walwala da bakin ciki irin na baya kenan.

Wanda kuma babu wanda yake marmarin komawa cikinsa. Idan mun kara komawa ga tarihi, za mu ga cewa Allah mabuwayi Ya azurta Babanmu Annabi Adamu da Hauwa’u. wadda ta yaye masa waccan damuwa. Amma sai Ya halicce ta da waccan suffa wadda ta sha banban da tasa. Wato tana da dabi’u da halayya akasin nasa. Haka nan suffar jikinsu daga gani za ka iya fahimtar alamun karfi da na rauni.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 3

Wannan tsari kuma da aka yi ta da shi, shi ne mafi dacewar tsari na abin da zai iya dauke masa kewa a wancan lokaci. Harwayau, shi ne dai tsari na macen da za ta iya dauke wa namiji kewa, cikakkiyar debe kewa har yau har gobe. Wannan shi ya sa har yanzu idan namiji yana son samun cikakkiyar debe kewa daga mace, dole sai ya rankwafo a wasu wuraren ya ajiye nasa tsohon tsarin, ya gauraya da nata.

Wato ba yadda yake mu’amula da maza ‘yan’uwansa ba. Kamar dai yadda a sama muka ce maza sun canza tsarinsu na win/lose bayan cakuduwarsu da mata. Daga muhimman abubuwan da mata suka manta a yau, akwai yanayin maraban da suka yi wa maza a wancan karni. Wato yayin da maza suka zo duniyar mata, sai suka taras da su sun yi wata da’ira, suna ta faman tattauna damuwarsu, wadda kuma sun gaza gano maganinta. Don haka suka tsaya daga nesa suna kallon su.

Domin ba su da tabbacin irin kallon da za su yi musu in sun karasa. Ko da matan suka hango su sai suka yi musu wata irin gayyata da kalmomin da suka tabbatar musu cewa lallai suna bukatarsu. “Ku zo, dama mun dade muna jiranku. Ku zo ku karfafe mu, domin mu ba mu da karfi. Ku zo ku nemo mana mafita. Tabbas haduwarmu da ku ce za ta zama silar rayuwar farin ciki” Abin mamaki yanzu shi ne, mata sun san yarda za su yi wa namiji irin wannan gayyatar a farkon soyayyarsu.

Amma da zarar sun kwana biyu a matsayin ma’aurata sai su manta yanda za su ci gaba da tura wa mazan irin wannan sakon gayyata. Yana da kyau mata su sani cewa, namiji yana samun cikakkiyar nutsuwa da yin zamantakewa da mace iyakar kokarinsa ne yayin da ta nuna masa tana bukatarsa, matukar bukata. Ta nuna masa tabbas in babu shi akwai matsala, ita ba za ta iya tafiyar ba. Amma da zarar mace ta nuna wa mijinta ba ta bukatar komai daga gare shi, ko ta nuna ko da shi ko ba shi ba ta da wata damuwa.

To daga sannan shi fa an dau hanyar kashe ruhin tabuka wani abin arziki a zamantakewa ko nuna soyayyarsa gare ta kenan. Wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa auren mace mai kudi da za ta rika daukar dawainiyar gida, armashinsa ba ya tsayi. Domin duk juyin da za a yi shi namijin ba zai iya sakin yi taka cikakkiyar rawar da ta dace namiji ya taka a gidansa ba.

Kasancewar wancan sako na gayyata ba ya zuwa zuciyarsa. Idan namiji ya rasa irin wancan gayyata daga mace, to zai koma ainishin tsarinsa na win/lose kenan, ko da kuma yana da mata hudu. Zai koma kansa kawai ya sani ba ruwansa da kowa. Mata da yawa ba su san cewa rashin aika irin wannan sakon ne ya zamar da mazansu ‘yan ko-in-kula ba. Daga cikin hanyoyin da namiji yake jin kansa a matsayin wanda yake cikin harkokin soyayya ko aure tsumdun, shi ne ya ga yana bayarwa.

Da yawa maza suna tsammanin bayarwa kamar sauke hakki da kyautatawa ce kawai. Amma anin da ba su sani ba shi ne, akwai nishadi mai girma a ciki. Amma da yawa ba sa fahimta sai sun tsinci kansu cikin kadaici. Wato bayan sun dena bayarwar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: