Wasanni

Yaya Gasar La liga Da El-Clasico Za Su Kasance Da Messi Da Ronaldo?

Kawo yanzu za a iya cewa hankalin duniyar kwallon kafa ya koma kan makomar La liga bayan rabuwa da dan wasa Messi, daya daga cikin shahararrun ‘yan kwallon da suka kayatar da duniya da kara wa gasar martaba a idon duniya.

A ranar Lahadi ce Messi cikin kuka ya yi bankwana da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da abokan wasansa da kuma magoya bayansa a Sifaniya bayan Barcelona ta yanke shawarar rabuwa da shi saboda ba ta iya biyansa kudin albashi.

Gasar La Liga da ake kira gidan Galacticos ta yi shura wajen tara zaratan ‘yan kwallon duniya musamman saboda karfin Barcelona da Real Madrid manyan kungiyoyin Sifaniya da ke hamayya da juna.

Ko da yake rabuwa da shahararren dan kwallo ba sabon abu ba ne a tsakanin Barcelona da Real Madrid domin zaratan ‘yan kwallon da Messi ya yi zamani da su sun riga shi sauya sheka daga La Liga.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun yi zamanin da tarihin gasar La Liga da hamayyar Barcelona da Real Madrid ba zai taba mantawa da su ba duba da irin bajintar da suka nuna wajen lashe kofuna da kyaututtuka daban-daban a tsakaninsu.

A shekarar 2018 dan wasa Cristiano Ronaldo wanda ya fi yawan cin kwallaye a tarihin Real Madrid tare da lashe kofin zakarun Turai sau hudu, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus, matakin da ya ja hankalin duniya. Kuma kamar Messi batun kudi na daga cikin dalilin da ya sa Ronaldo ya bar La Liga zuwa Seria A.

Hamayyar a La Liga ta yi zafi zamanin BBC (Benzema da Bale da Cristiano) a Real Madrid da kuma MSN (Messi da Suarez da Neymar) a Barcelona kuma an buga wasa mai kayatarwa tare da samun nasara mai ban mamaki hadi da rikici musamman a lokacin da ake buga wasan hamayyar na El-Classico.

Yanzu dan wasa Karim Benzema da Suarez kawai suka rage a gasar La liga, dan wasa Benzema yana kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sannan shi kuma Luis Suarez a kungiyar Atletico Madrid.

Sai dai duk da rabuwa da Ronaldo da sauran zaratan ‘yan kwallo zamanin BBC da MSN, gasar La liga ta ci gaba da armashi saboda Messi saboda yadda ya ci gaba da nuna gwarzantaka da taimakawa Barcelona wajen lashe gasar La liga.

Hamayya ta koma tsakanin dan wasa Messi da Sergio Ramos tsohon kaftin din Real Madrid, bayan tafiyar Ronaldo sai dai Ramos ya koma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German a watan Yunin shekara ta 2021 bayan shekaru 16 a Real Madrid.

Amma yanzu an wayi gari a gasar La liga babu dan wasa Leonel Messi babu Cristano Ronaldo da Sergio Ramos kuma babu tabbas kan wasu ‘yan kwallon da za su gaje su domin armashin gasar.

Messi ya lashe wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kofuna 35 kuma dan wasan mai shekara 34 a duniya, ya shafe shekara 21 a Barcelona tare da lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya sau shida sannan ya ci wa Barcelona kwallaye 672 a wasanni 778, tare da lashe wa kungiyar kofuna 35.

Sai dai masu sharhi a kan kwallon kafar Turai na ganin rashin dan wasa Messi zai rage wa La Liga daraja da armashi, amma shugaban kula da gasar La liga Jabier Tebas ya ce tafiyar kaftin din na Barcelona da Argentina ba zai sauya komai ba.

Tebas ya ce gasar ba za ta dogara a kan wani dan wasa ko wata kungiya ba, yana mai cewa fitattun ‘yan wasa da dama sun tafi kuma ba abin da ya canza inda ya bayar da misali da dan wasa Cristiano Ronaldo da Neymar yana mai cewa sun tafi amma gasar Seria A da League 1 da suka koma ba za ta iya gogayya da La Liga ba.

A cewarsa gasar Premier ta Ingila ita ce mafi shahara a duniya kuma ta samu wannan girman ne ba tare samar da gwarzon dan wasan duniya ba sannan ya cigaba da cewa duk da abokan hamayyar La Liga za su yi murnar tafiyar Messi amma yana da tabbacin hakan ba zai sauya komai ba.

Sai dai kuma yawancin masu sharhi da masu bibiyar kwallon kafa na ganin rabuwa da Messi babbar hasara ce ga martabar La Liga kuma wasunsu na ganin La Liga za ta samu nakasu a kudaden shigarta. Kuma La Liga za ta rage karfi idan aka kwatanta da Seria A mai Ronaldo da kuma gasar da za ta yi babban kamun Messi.

Sannan za a iya cewa Sergio Baskuet da Pikue da Alba da Roberto ne ‘yan wasan da za su jagoranci tawagar Barcelona bayan tafiyar Messi wanda hakan ya sa ake ganin duk da haka abu ne mai wahala tasirinsu gaba daya ya kai na Messi.

Dubban magoya bayan Barcelona ne suka mamaye harabar gidan Messi domin fatan yin tozali da gwaninsu domin su yi masa bankwana kuma an nuna hotunansu sanye da riga mai lamba 10 ta Barcelona.

Ana ganin dimbin magoya bayan Barcelona za su ci gaba da goyon bayan Messi wanda ya lashe masu duk wani kofi da suke bukata a kwallon kafa sai dai a ranar Juma’a za a soma La liga, kuma masu sharhi na ganin rashin Messi wani wagegen gibi ne a Barcelona Amma duk da haka Barcelona ta fara rayuwa babu Messi a ranar Lahadi kuma ta fara da kafar dama.

Barcelona ta doke kungiyar Juventus ci 3-0 a gasar lashe kofin Gamper, wasan share fagen kaka da suka fafata. Kuma Sabon dan wasa Memphis Depay ne ke ci gaba haskakawa a wasannin share fagen kaka inda ya zura kwallo a ragar Juventus ana minti uku da soma wasa.

Wannan kan iya zama wata babbar dama ga ‘yan wasa masu tasowa, wadanda sakamakon Messi ba a basu dama domin nuna bajntarsu ba kuma hakan yana nufin nan gaba kadan za a samu matsan ‘yan wasa masu tasowa.

Kawo yanzu dai sai an fara buga wasannin La liga sannan za a gane karfin kungiyoyin ne ta hanyar gasar cin kofin zakarun turai wanda shi ma za a fara bugawa a watan gobe mai kamawa kamar yadda hukumar kwallon kafa ta Turai ta tabbatar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement