
annan biri wanda ake kira orangutan a Ingilishi yana da wata halitta ce mai kama da faifai a gefen kumatunsa, wadda mata ke sha’awa, amma kuma sai namiji ya kai shekara 20 take fito masa.
Melissa Hogenboom ta yi nazari.
Duk balagaggen nau’in wannan biri na orangutan, wanda ake samun irinsa asali a kasashen Indonesia and Malaysia yana da wannan abu mai kama da faifai, kuma matan birin sun fi kaunar wanda yake da shi kan wanda ba shi da abin.
Cikakken balagaggen birin ya kai tamata biyu a girma kuma yana da babban makoko (a makogaro) wanda dukkanin wadannan alama ce ta iko da kuma karfi.
Sai dai wadannan abubuwa sukan dauki lokaci kafin su fito wa namijin.
Wani yakan kai shekara 20 kafin wannan abu mai kamar kunne ko mahuci ya fito masa a gefen kumatu.
Mazan da wannan abu bai fito musu ba, sukan yi kama da mata kuma ba su kai wadanda na su ya fito ba girma.
Wani sabon bincike ya yi kokarin bayyana dalilin da ya sa abin ya kan dauki lokaci kafin ya fito wa mazajen.
Mata sun fi son mazan da suka fi fadin fuska
Domin gudanar da wannan bincike masana kimiyyar, sun tattara kashin mazajen wannan nau’in biri guda 17.
Goma daga ciki wadanda wannan abu ya fito musu ne, shida kuwa ba su da shi, yayin da sauran dayan ya fara fito masa.
Dukkanninsu suna gandun daji ne na Mawas da ke Kalimantan a Indonesia.
Masanan sun duba yawan kwayoyin halitta a cikin kashin birran, inda suka gano wadanda suke da wannan halitta ta gefen kumatun suna da yawan kwayoyin halitta na jima’i na namiji (testosterone) a cikin kashin nasu.
Jagoran masi binciken Pascal Marty na jami’ar Zurich a Switzerland, ya ce, ” mazan da wannan abu mai kama da mahuci bai fito musu ba ba su da yawan kwayoyin jima’i na namiji a cikin kashin nasu”.
An wallafa wannan bincike ne a mujallar, ”American Journal of Primatology”.
Baligan maza sun fi mata girma
Da zaran mazajen sun fara fitar da wannan halitta ta gefen kumatun mai girma sai yawan kwayoyin halittarsu na jima’i ya karu.
”Yawan wannan kwayoyin halitta a jikin irin wadannan mazaje da ake wannan nazari a kansu ya dan bayar da mamaki, amma ya nuna bukatar samun karin kwayoyin halittar jima’in domin bayyanar sauran alamu na balaga (kamar wannan abu na gefen kumatu),” in ji Marty
Idan namijin birin ya samu cikakkiyar wannan halitta sai kuma yawan kwayoyin halittarsa na jima’i su sake karuwa.
Wani nazari da aka yi na baya a kan irin wadannan birrai da ke gidan namun daji ya nuna cewa gasa tsakanin mazaje na iya sa wannan halitta kara girma.
Haka kuma wani nazarin na baya ya nuna cewa gasa tsakanin mazaje na iya haddasa gajiya a tsakaninsu wadda kuma ka iya dakushe girman wannan halitta a mazan da ba su da karfi sosai.
Sai dai binciken Marty bai samu shedar da ke tabbatar da hakan ba.
”A wurin da muke gudanar da bincikenmu ba mu taba ganin lokacin da wasu mazaje baligai masu wannan halitta ta gefen kumatu suke fada ba.
Saboda haka ba mu da shedar da ta nuna gogayya tsakanin mazajen na da nasaba da ya karin yawan kwayoyin halitta,” in ji masanan.
”Sakamakon wannan binciken ya sa mu yi watsi da maganar cewa damuwa ko hamayya ita ce babbar abar da ke sa dakushewar girman wannan halitta ta gefen kumatun birran.”
Wasu mazajen ba su da sa’ar samun wannan halitta ta fuska
Bayan farin jini a wurin mata, bincike ya nuna cewa wadanda suke da wannan halitta babba a kumatun nasu sun fi koshin lafiya.
Wadanda suka tsufa da kuma masu rauni ana ganin wannan halitta ta motse a jikinsu.
Girman wannan halitta na nunawa karara cewa abu ne da ya dogara ga sauyin kwayoyin halitta.
Amma ”abin da ke haddasa wannan sauyi shi ne har yanzu ba a gano ba,” in ji Marty.
Yana ganin wadanda suka yi bi diddigin rayuwar wannan nau’i na biri (orangutan) gaba dayanta watakila su iya gano amsar.
Idan ana son karanta wannan a harshen Ingilishi a latsa nan
Add Comment