Kiwon lafiya

Yawan Amfani Da Shafukan Sada Zumunta Na Hana Bacci

Akwai yiwuwar cewa matasan da ke kashe sama da awa uku a rana a kan shafukan sada zumunta ba za su yi bacci ba sai bayan karfe sha daya na dare kuma za su iya farkawa cikin daren, in ji wani bincike da aka gudanar a Birtaniya.

Wannan na shafar matashi daya cikin uku- inda matashi daya cikin biyar ke kashe sa’o’i biyar ko fiye a manhajoji kamar su Instagram da Whatsapp da Facebook kullum, a cewar binciken.

Masu bincike a jamai’ar Glasgow sun ce akwai yiwuwar cewa matasa ‘yan shekara 13 zuwa 15 na jan kafa wajen kwanciya bacci saboda suna amfani da wayoyinsu.

Likitocin lafiyar kwakwalwa sun ce a daina amfani da waya awa daya kafin a kwanta bacci.

Sai dai binciken da aka gudanar na matasa 12,000 ya gano cewa hana matasa amfani da waya zai iya zama babbar matsala saboda lokaci ne na cin gashin kansu, lokaci mai muhimmanci da suke zumunci da abokansu.

Binciken ya kara tabbatar da wani hasashe na cewa lokacin da matasa ke batawa a kan shafukan sada zumunta na rage lokutan da suke dauka suna bacci- kuma rashin bacci na tasiri a kan lafiyar kwakwalwa da kokarin makaranta.

Sa’o’i nawa matasa ke kashewa a shafukan sada zumunta?

Sa’o’i a rana Kashin matasa maza Kashin matasa mata Kashin duka matasa
Kasa da sa’a daya 43.8 22.8 33.7
Tsakanin sa’a daya da sa’o’i uku 32.1 31.1 31.6
Daga sa’a uku zuwa biyar 10.4 17.7 13.9
Sama da sa’a biyar 13.7 28.4 20.8

‘Kar a yi ba su’

Dakta Holly Scott ta bangaren ilimin halayyar dan Adam na Jami’ar Glasgow, ta ce binciken bai iya tabbatar da cewa yawan amfani da shafukan sada zumunta na jawo rashin isasshen bacci ba, amma da alama yana takara sosai da bacci.

“Matasa na iya kwanciya amma idonsu biyu saboda basu shirya yin baccin ba kuma suna fargabar cewa idan suka yi bacci suka fita daga shafukan za a yi ba su”

Dakta Max Davie ta Kwalejin lafiyar yara ta ce isasshen bacci mai inganci na da muhimmanci ga yara da matasa.

“Muna bayara da shawarar cewa matasa sun daina amfani da wayoyinsu a kalla awa daya kafin su kwanta bacci saboda kwakwalwarsu ta samu ta huta.

“Rashin bacci na da mummunan tasiri ga lafiyar matasa da dangantakarsu da sauran ‘yan uwansu da abokansu da kuma kokarinsu a makaranta.”